Refugee Report

“Open your eyes – hear my voice!”

This is not right, isn’t it?

listen on Soundcloud

2014/06/05 05:15

Aus Niger, seit 2 Jahren in Deutschland; Berlin [12-02-2014]

HAUSA:

Barka da wuni. Ku wanda kuke k’ok’ari cikin taimaka wa wanda suka zo, suke k’asa da ku, da wad’anda kuke ganin za ku iya taimaka mini, da yake ma jiya na yi magana game da abin da yake damu na. Ina da laifin da ban san shi ba kuma laifin ba na hannun hukuma ba ne. Ba wai ina da karambani ko b’atanci ba ne, a’a sai dai ban sani ba, hak’uri nake so a yi mini fa, a gyara mini. Tun da na shigo Germany yau wata bakwai ana yi mini tara ne. Kowane lokaci ina biyan tara ne. Wannan tara ko na mene ne, ban sani ba, saboda ba ni harkar duruk, ba ni mafiya, amma dai ni zaunawa ne ban iya ba wuri guda. Kullum ina tafiya shi ya sa, don haka ina da laifi da kowane Lokaci ana yi mini tara da ya danganci haka. Gaskiya ne. Kuma ina da labarin kuna taimaka wa mutane, Kuna taimaka wa bayin Allah. To, don Allah mu ma ku taimaka mana cikin haka don mu tsere da mutuncinmu haka. Ya kamata a ce.......mun kai da mu yi aure ba mu yi auren ba. Ba mu da shi, Kuma muna da doka wanda ya zama dole cewa, inda aka ajiye ka nan za ka tsaya. Gaskiya yana da kyau inda aka ajiye mutum ya tsaya wurin nan, to amma ka sani an kai ka wurin da wani ba ya son ka. An kai ka wurin da wani ba ya son ka, ba ka iya zama tare da wanda ba ya son ka. Mutum zai biyo ya ce zai yanka ka ko ya ce zai yi harbi. Ka ga kai wannan ba ka iya ka zauna da shi ba, Ko ba haka ba? Yanayi don saboda nan ne ake samun had’ari. Mutumin da dai ba ka masa kome ba, ya doke ka, ka ga shekaranjiya yanda aka yi wa wani. An sa masa yatsa a ido ana so a kashe shi. Ka ga ba tsari ba ne. Ai ba kowane lokaci mutum yake tafiya tare da hukuma ba. Shi ne ya sa abin da nake so don Allah ku taimaka mana. Abin da za ku iya yi game da takardarmu, takardu da harkokin lauya, muna so. Ba ni da lauya ne. In za ku iya ba ni lauya. Takardana ma tana hannun hukuma, tun da na shigo Germany sun amshi takardana yana hannunsu kuma yanzu takardar ya kamata a ce ina tare da shi. Ba ka sami takardar Germany ba ma, naka da kake da shi ya b’ace. Ka ga wannan bai yi ba. Ko ba gaskiya ba? Amma don Allah ku taimaka mini da lauya da kuma irin abin da yake faruwa tsakani na da wanda suke rik’e da ni. In za ku iya taimaka mini ku kama mini takardana yana wurinsu. Yanzu ina buk’atar takardar. Ba ni da takarda kuma wanda suka ba ni, kullum in sun gamu da ni suna rubuta mini tara. Ka ga wannan bai yi ba, ko ba haka ba? In kuma kuna da aiki da kuke iya taimaka mana da shi, to sai ku taimaka da shi. Kowane irin aiki ne: na hannu ne, aikin k’arfi ne, in na limi ne ma, kai kowane iri in dai aiki ne kuna da wanda za ku taimaka mana da shi, za mu yi. Kun gane? Kuma mun san ko mene ne tsarin rayuwar, dole sai a hankali ne. Sai ku yi hak’uri da abin da muka sani da wanda ba mu sani ba, saboda mun shigo Europe kuma a cikin Europe muke nan Germany. Ku ne za ku gyara ta don ku kuke gyara ta. K’asarku ne, ku za ku shiga gaba kuma abin da ba mu sani ba, za ku iya taimaka mana da shi cikin haka. Abin da za ku yi saboda......Haka dai za a ce. Ni dai abin da na sani ke nan. Takardana yana hannun hukuma. Yanzu ni ban san lauyan da…..ba ni da lauya, ban san lauyan da zan d’auka wanda zai je ya mini ba. In ku kun sani, za ku taimaka mini da lauya, sai ku ba ni lauya wanda zai shiga mini gaba bisa takardana da kuma irin tarar da ake mini yau wata bakwai ko takwas ne nake cikin Germany kuma ni kowane wata ina da tara, ina da letter, kowane wata ina da letter. Kowane wata ina da letter biyu ko uku saboda haka hankalina ya tashi, Allah hankalina ya tashi. Wannan abu idan na tuna shi, sai in rasa ina ne zan sa kaina. Yana daga cikin abubuwan da suke d’auka mini hankali daga nan Turai. Ba ka da aikin yi kuma sai ana maka tara kullum. Ka ga wannan shi ma ba zai bar ka ba ai. Wani abu ne wanda zai iya zama a cikin.......ai ba za ka ce kana wani rayuwa mai kyau ba kuma da kwanciyar hankali. Ko dai ma mene ne, haka ne muke tafiya da shi.

ENGLISH:

Good afternoon. You people who are making efforts to assist (those refugee) who came and are (kept) under your care, and those who are in the position to assist me can do that. I have already complained about my predicament yesterday. I have a case, which I do not understand. However, the case is not with the authority. I am not trying to interfere or implicate (someone) no, I only want the authority to be patient with me and correct my faults. Since I came to Germany for the past seven months, I have been paying fines every time and I do not know the reason for the fines. I am not involved in selling drugs neither am I a member of a mafia group. However, I do not remain in one place, every time I am on transit, may be that is why I am at fault all the times and in relation to this, I am being fined. In fact I am aware that you are assisting people, you are assisting (those) innocent people. Therefore, please kindly assist us also in this problem so that we can maintain our reputation. It is suitable that…….it is high time we got married, but we are not married, yes not yet married. There is a law binding on us and it makes it compulsory on us to remain where we are camped. Indeed, it is good for someone to remain in his camp, but you should know that one is camped in a place where there is someone who does not like him. When you live in a camp where someone does not like you, I mean you cannot live together with someone who does not like you. Someone can come around and say he will kill you or he will say he will shoot. You know you cannot live with such a person, isn’t it? There is a serious danger in this kind of situation. There is no justification when someone beats you without a cause. You can see what happened to someone just two days ago. He was poked in the eye in an attempt to kill him. This is not good. One does not walk around all the times together with a policeman. This is why I want you to help us for God’s sake. We shall appreciate what you can do for us concerning papers, yes papers and lawyers. My paper is with the police / authority. They confiscated my paper since my arrival to Germany. It has been with them while it is supposed to be with me. Look at it, you have not secured the German papers / Pass and the one which you had got lost / confiscated. This is not right, isn’t it? But please assist me with a lawyer and the type of thing which is happening between me and those who are detaining me. Help me and get my paper from them. I need the paper now because I do not have paper. The one they gave to me is equivalent to nothing because any time I meet the security personnel, they fine me. This is not good, isn’t it? And if you have a job which you can offer to us, please give it to us. Any type of job: craft, manual job, office job or just any type in as much as it is a job, give us and we shall do it. Do you understand? We know the life style. It must be slowly therefore, you have to be patient regarding what we know and what we do not know because we came to Europe and we are now in Europe precisely in Germany. It is you people who will amend the system because you are the ones who are supposed to work towards amending it. It is your country therefore, it is you who will stand for us and enlighten us on what we do not know in this matter. What you can do because of……..This is what to say, as far as I am concerned, this is what I know. My paper is with the police / authority. To date I do not know a lawyer who……..I do not have a lawyer, I do not know the lawyer who can defend me. If you people know and you can help me with a lawyer, then give me who can stand for me concerning my paper and the fine which I have been paying for the past seven to eight months I have been in Germany. I pay fine every month and I receive letter. Every month I receive letter. Every month I receive two or three letters, as such I am worried, I swear I am worried. Any time I remember this matter, I do not know where to take myself (for comfort). It is one of the things that disturb my peace in Europe: You do not have job and you are being fined every now and then. This situation will never give you peace of mind. It is something that can remain in…….You cannot say you are living a good life with peace of mind. Anyway, no matter what is the situation, this is how we are surviving.

Transcription and translation by Yusuf Baba Gar. Thank you.

back